Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Dakile Harin ISWAP Kan Sansanin Soji A Borno, Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama

Published

on

FB IMG 1765628717619

Dakarun sojin Najeriya karkashin rundunar Operation Hadin Kai sun dakile wani hari da ‘yan ta’addan ISWAP suka kai kan wani sansanin soji a yankin Mairari na Jihar Borno, inda rahotanni suka ce an kashe ‘yan ta’adda da dama.

A cewar wata sanarwa da Jami’in yada labarai na Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Laftanar Kanal Sani Uba, ya fitar a ranar Asabar, harin ya faru ne daga daren 12 zuwa safiyar 13 ga Disamba, 2025.

Advertisement

Sanarwar ta ce ‘yan ta’addan sun yi yunkurin kutsawa cikin sansanin ta hanyar amfani da motoci biyu dauke da bama-bamai (VBIEDs), amma dakarun sojin sun gano su tun kafin su isa sansanin, inda suka lalata motocin tare da dakile harin.

Ina Nanata Cewa Babu Kisan Gilla Kan Kiristoci Ko Musulmi A Najeriya — Shugaba Tinubu 

Rundunar ta ce hotunan CCTV da bayanan da aka tattara daga wurin sun nuna cewa an kashe wasu daga cikin ‘yan ta’addan, yayin da wasu suka jikkata kafin su tsere daga yankin.

Advertisement

Bayan faduwar harin, dakarun sojin tare da hadin gwiwar ‘yan sanda na musamman da kuma Civilian Joint Task Force (CJTF) sun gudanar da bincike a yankin, inda suka gano gawawwakin ‘yan ta’adda da kuma kwace makamai da kayan aiki.

Daga cikin kayayyakin da aka kwato akwai bindigogin AK-47, harsasai, gurneti, babura, na’urorin sadarwa, kayan yaki da kayan agajin jinya.

Advertisement

Sojojin sun jaddada cewa za su ci gaba da yaki da ‘yan ta’adda domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.

 

Advertisement

 

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending