Politics
Hon. Da’u Aliyu Abubakar Ya Kai Ziyara Ga Manyan Shugabannin APC Domin Tattauna Makomar Jam’iyya A Kano
Hon. Da’u Aliyu Abubakar, wanda aka fi sani da Kogunan Kasar Hausa, ya kai ziyarar ban-girma ga manyan shugabannin jam’iyyar APC domin ci gaba da neman hadin kai da tattaunawa kan makomar jam’iyyar a Kano da ma kasa baki daya.
A cikin jerin wadanda ya ziyarta akwai tsohon shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, tare da shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Hon. Abdullahi Abbas.
Hakanan ya ziyarci tsohon dan takarar mataimakin gwamnan Kano, Hon. Murtala Sule Garo, da kuma tsohon shugaban Karamar Hukumar Birni, Hon. Muntari Isaq Yakasai.
Wasu fitattun jiga-jigan jam’iyyar da suka halarci tattaunawar sun hada da:
Hon. Faizu Alfindiki
Hon. Baffa Babba Dan’Agundi
Amb. Kabiru Rabiu
Alh. Nasiru Aliko Koki
Shugaban APC na Karamar Hukumar Birni, Alh. Sani Fata Sharada
Tsohon dan majalisar jiha na Birni, Hon. Salisu Ahmad Gwangwazo
Ziyarar ta mayar da hankali ne kan tattauna hanyoyin kara karfafa jam’iyyar APC a jihar Kano, tare da duba dabarun da za su inganta hadin kai da ci gaban jam’iyyar a matakin jiha da kasa.
Wannan ganawa, in ji wasu da suka halarta, na daga cikin jerin kokarin da ake yi na ganin jam’iyyar ta kara samun daidaito da kuzari wajen shiryawa manyan kalubalen siyasa da ke tasowa a jihar Kano.
