Connect with us

Sports

Za’a Gudanar Da Wasa Da Baburan Biker Sama Da 300 A Kano

Published

on

Bikers Association of Nigeria
Spread the love

Kungiyar Kano United Biker ta sanar da shirinta na karɓar bakuncin babban taron masu tuƙa Baburan Biker mai suna “The Gathering 2025”, wanda za a gudanar a birnin Kano daga ranar 1 zuwa 4 ga watan Nuwamba, 2025.

Shugaban Kwamitin Shirya Taron (LOC), Mohammed Rabiu Abubakar, ya bayyana wa manema labarai cewa taron zai samu halartar sama da ’masu tuƙa Baburan Biker 300 daga sassa daban-daban na Najeriya da wasu ƙasashen Afrika da Turai.

’Yan Yahoo’ Matasa Ne Masu Basira Da Suke Bukatar Shiryarwa Ba La’anta Ba —Peter Obi

Taron The Gathering 2025 zai haɗa da tseren babura, wasanni, nune-nunen al’adu, da kuma tattaunawa kan hanyoyin bunƙasa yawon buɗe ido a Najeriya.

Hakazalika, kungiyar ta bayyana shirye-shiryen ayyukan jin kai da za a yi a lokacin taron, ciki har da:

Advertisement

Kai tallafi gidan marayu a Kano;

Mika tallafin magunguna zuwa Asibitin Asiya Bayero;

Ziyartar Gidan Sarki da Gidan Makama domin karfafa hulda da shugabannin gargajiya.

Abubakar ya tabbatar da cewa an samu izini da goyon bayan hukumomin tsaro da na zirga-zirga a jihar Kano, wanda zai tabbatar da gudanar da taron cikin tsari da kwanciyar hankali. An kuma tsara matakan tabbatar da lafiyar mahalarta da rage cunkoso yayin tseren babura.

Advertisement

Taron zai ƙare ne da Culture Costumed Gala & Award Night, inda za a karrama fitattun ’yan babura da kungiyoyi da suka ba da gudummawa wajen bunkasa harkokin babura da al’adu.

Shugabannin Kano United Biker sun bayyana fata cewa taron zai janyo hankalin masu yawon buɗe ido, kawo tallafi ga al’umma, kuma ya ƙara haska suna da al’adun Kano a idon duniya.

Advertisement