Connect with us

News

HAJJIN 2026: NAHCON Ta Sanar Da Buɗe Shafin Ɗaukar Ma’aikatan Wucin Gadi Na Kiwon Lafiya

Published

on

Zazzabin Lassa Cutar ta yi Ajalin Mutum 118 A Cikin Watanni Uku

Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) na sanar da jama’a musamman ƙwararrun ma’aikatan lafiya Ƴan Najeriya, cewa za a buɗe shafin ɗaukar ma’aikatan wucin gadi na kiwon lafiya (National Medical Team – NMT) don Hajjin 2026 a hukumance a shafin yanar gizon NAHCON.

Ana gayyatar ma’aikatan lafiya da suka haɗa da likitoci, masana hada magunguna (pharmacists), nas-nas (nurses), da ma’aikatan kula da lafiyar muhalli su gabatar da kansu ta hanyar cika fom a shafin intanet da aka tanada. Shafin zai buɗe daga 11:00 na dare, 12 ga Disamba, 2025 zuwa 11:59 na dare, Litinin 15 ga Disamba, 2025.

Advertisement

RIKICIN KAN ASALIN MAHAIFI: An Hallaka Uwa Da Jaririnta Ɗan Wata 10, An Jefa Su Rijiya A Katsina

A lura cewa duk masu nema dole ne su kasance suna aiki a yanzu haka (active service) a lokacin cika fom ɗin, kuma ba su yi aikin wucin gadi na kula da kiwon lafiya a Hajjin uku da suka gabata ba wato daga (2023, 2024 da 2025). Don ƙarin ka’idoji da za a cika, ana shawartar masu nema su ziyarci shafin yanar gizonna hukumar NAHCON a nahcon.gov.ng

Bayan haka ana kira ga duk waɗanda za su cika fom ɗin don neman aikin su tabbata sun karanta sharuddan da aka gindaya, da kuma tabbatar da sun cika su domin gujewa rashin kai wa ga nasara.

Advertisement

NAHCON za ta ci gaba da sanar da jama’a game da shirye-shiryen Hajjin 2026.

 

Advertisement

 

PREMIUM TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending