News
Kotun Daukaka Kara Ta Yi Watsi Da Bukatar Hana Jami’an Gwamnati Neman Lafiya A Kasashen Waje
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Kotun daukaka kara ta Nijeriya ta yi watsi da bukatar hana jami’an gwamnati fita kasashen waje don neman lafiya, bukatar da babban lauya kuma ɗan gwagwarmaya, Femi Falana (SAN), ya shigar.
Falana ya daukaka karar ne bayan da babbar kotun jihar Lagos da ke Ikeja ta ki amincewa da bukatar da ke neman tilastawa gwamnatin tarayya ta gyara asibitocin cikin gida, tare da dakatar da jami’an gwamnati daga tafiya kasashen waje don neman lafiya.
Yadda Faɗuwar Farashin Gas Din Girki A Kano Ya Jawo Dogon Layi A Lokacin Azumi
Babban lauyan ya bayyana cewa irin wannan mataki zai tilasta wa gwamnati maida hankali kan inganta harkar lafiya a cikin gida, domin amfanin ‘yan kasa gaba ɗaya.
Sai dai kotun daukaka kara ta yi watsi da bukatar, tana mai bayyana cewa ba ta da hurumin hana mutum walwala ko yancin neman lafiya a duk inda ya ga dama.
Falana dai na daga cikin manyan ‘yan gwagwarmaya da ke fafutukar ganin an gyara asibitocin Nijeriya domin rage dogaro da kasashen waje wajen kula da lafiyar jami’an
gwamnati.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
