Connect with us

News

Rikici Ya Barke A Jihohi Da Dama Kan Aiwtar Da ‘Yancin Cin Gashin Kai Na Kananan Hukumomi

Published

on

Rikici ya barke a jihohi da dama kan ‘yancin cin gashin kai na kananan hukumomi

 

Bayan hukuncin Kotun Koli da ya ba wa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu, rikici ya barke a jihohi da dama sakamakon sabani kan yadda za a aiwatar da hukuncin.

Advertisement

Hukuncin da Kotun ta yanke a ranar 11 ga watan Yuli, 2024, ya tabbatar da cewa gwamnatocin jihohi ba su da ikon rushe shugabannin kananan hukumomi da aka zaba a bisa doka.

Kotun Daukaka Kara Ta Yi Watsi Da Bukatar Hana Jami’an Gwamnati Neman Lafiya A Kasashen Waje

Sai dai, bayan watanni takwas da yanke hukuncin, wasu gwamnatocin jihohi na jan kafa wajen aiwatar da umarnin, lamarin da ya haddasa rikice-rikicen siyasa da rasa rayuka a wasu yankuna.

Advertisement

A jihohin Osun da Rivers, an samu zanga-zangar jama’a da kuma baraka tsakanin mambobin jam’iyyun siyasa kan yadda za a dawo da zababbun shugabannin kananan hukumomi da aka rushe.

Masana na ganin cewa rashin aiwatar da hukuncin na barazana ga dimokuradiyya, yayin da ake kira ga gwamnati da ta tabbatar da bin doka da oda domin kawo karshen tashin hankali.

Advertisement

A halin yanzu, ana sa ran Majalisar Dattawa za ta shiga tsakani domin shawo kan matsalar.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending