Connect with us

Sports

NPFL Ta Ci Katsina United Tarar Naira Miliyan 9

Published

on

G5Py l XMAA0uP 1140x762
Spread the love

Hukumar dake shirya gasar Firimiya ta Najeriya (NPFL) ta ɗauki tsauraran matakai kan ƙungiyar Katsina United, inda ta ci ta tarar Naira miliyan tara, sakamakon tashin hankali da aka samu a wasansu da Barau FC a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina.

Harin ya faru ne a ranar Asabar, lokacin da ƙungiyar Barau FC ta farke ƙwallo, matakin da ya fusata wasu magoya bayan Katsina United, suka kutsa cikin filin wasa, suka soma far wa ’yan wasa da jefa abubuwa.

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Kebbi Ya Kuɓuta Daga Hannun ‘Yan Bindiga

A yayin rikicin, ɗan wasan Barau FC, Abraham, ya samu mummunan rauni a wuyansa, lamarin da ya tilasta dakatar da wasan na ɗan lokaci, tare da jefa ’yan wasa da jami’an wasa cikin firgici.

Cikin wata sanarwa da NPFL ta fitar, hukumar ta bayyana cewa ta same Katsina United da laifuka da suka haɗa da Gazawar hana magoya baya kutsa kai cikin fili,Jefa abubuwa cikin filin wasa,Haddasa hargitsi da ya kawo cikas ga gudanar da wasa,Rashin samar da tsaro mai inganci.

Advertisement

Saboda haka, hukumar ta yanke hukuncin kamar haka ₦1m a matsayin tarar cin zarafin dokokin wasa,₦2m kan gazawar samar da tsaro,Karin biyan gyaran motocin Barau FC da aka lalata,Wanda hakan ya kai jimillar tarar ₦9m.

 

 

Bugu da ƙari, NPFL ta umurci Katsina United da ta karbi bakuncin sauran wasannin gida a Jos, jihar Filato, maimakon filinsu na Katsina, har zuwa ƙarshen kakar wasa ta bana.

Advertisement

Hukumar ta kuma bai wa kulob ɗin sa’o’i 48 domin ɗaukaka ƙara idan ba su gamsu da hukuncin ba.

Matakin hukumar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ƙoƙarin tsaftace gasar ta Najeriya daga matsalolin tashin hankali da rashin bin dokoki, domin kare lafiya da martabar ƙwallon ƙasar.

 

LEADSHIP

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *