News
DA DUMI-DUMI: Sabon tsarin karban kudi a kanta ya fara aiki.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Babban bankin Najeriya (CBN) ya umurci bankunan kasuwanci da su fara biyan kwastomominsu Akan kanta saboda matsalar cinkoso a Layin ATM.
Babban bankin Najeriya ya fitar da wannan sanarwar a ranar Alhamis A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis. Inda Babban bankin, CBN ta ce, wannan sabon umarnin shi ne mafita,
Daliban makaranta sun kai wa ‘yan sanda hari bayan kashe abokin karatunsu
don rage kalubalen da ‘yan Najeriya ke fuskanta ta hanyar samun sabbin takardun kudi, da kuma rage layukan da ake samu a na’urar tantance kudi (ATMs) a fadin kasar.
Wannan sabon ci gaba ya zo ne a matsayin daya daga cikin sauyi da CBN ya yi tun bayan da ya bayyana manufar sake fasalin naira a watan Oktoban bara.
