Connect with us

News

Babu Ranar Daina Amfani Da Tsoffin Takardun Naira A Najeriya —Bankin CBN

Published

on

Gwamnatin Tarayya, Jihohi, Kananan Hukumomi Sun Raba Naira Tiriliyan 1.289 a Cikin Watan Satumba

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Babban Bankin Najeriya CBN ya ƙaryata labarin da ke yawo cewa za a daina amfani da tsoffin takardun Naira 200 da Naira 500 da kuma Naira 1000.

Advertisement

CBN ya buƙaci ’yan Najeriya su yi watsi da rade-radin, wanda ya ce ba su da tushe.

Babu Minista Ko Babban Jami’in Gwamnati Da Zai Yi Amfani Da Motoci Fiye Da 3 A Tawagar Sa —Shugaba Tinubu

Sanarwar da mai magana da yawun CBN, Hakama Sidi ta fitar ta ce har yanzu umarnin Kotun Ƙoli na ci gaba da amfani da tsofaffi da sabbin takardun Naira a tare nan yana aiki.

Advertisement

 

Ta ƙara da cewa har gobe CBN Bai janye umarni da ga bankuna da sauran cibiyoyin hadahadar kuɗaɗe na ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin da aka sauya wa fasali ba.

Advertisement

A ranar Juma’a ne aka baza rade-radin cewa daga ranar 31 ga watan Disamba za a daina amfani da tsofaffin takardun kuɗi na Naira 200 da Naira 500 da kuma Naira 1,000 a koma amfani sababbin da aka sauya wa fasali.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending