Connect with us

News

Rundunar Anti-Phone Snatching Ta Kama Mutane 10 Bisa Zargin Satar Wayoyi A Kano

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Rundunar tsaro ta Anti-Illicit Drugs and Phone Snatching Force a Kano, mai yaƙi da faɗan daba, fashi da ƙwacen waya da kuma safarar miyagun ƙwayoyi, ta kama mutane 10 bisa zargin satar wayoyin hannu da kuɗaɗen jama’a a kasuwar Bata zuwa Ƴan Kura da ke jihar Kano.

Kwamandan rundunar, Nura Salisu Sharaɗa, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Litinin, 2 ga Nuwamba, 2026.

Gwamnatin Sakkwato Ta Rufe Ofishin Kamfen Jam’iyyar ADC

Ya ce rundunar ta samu bayanan sirri kan yawaitar satar wayoyi da kuɗaɗe a kasuwar Bata zuwa Ƴan Kura, lamarin da ya sa ta tura jami’an Operation Phone Snatching ƙarƙashin jagorancin Bala Abubakar domin gudanar da bincike da cafke waɗanda ake zargi.

A cewarsa, jami’an sun samu nasarar cafke mutum 10 a yayin samamen da suka gudanar a kasuwar da kewaye.

Waɗanda aka kama sun haɗa da Sani Ibrahim, mai shekaru 27, mazaunin Fagge; Abdullahi Sani, mai shekaru 12, mazaunin Rijiyar Lemo; Auwalu Sadik Gyaranya, mai shekaru 23; da Yusuf Idris, wanda aka fi sani da Ɗan Kunne, mai shekaru 21, mazaunin Burget.

Advertisement

Sauran sun haɗa da Nura Adamu, mazaunin Rimin Keɓe; Aminu Muhammad, mai shekaru 21, mazaunin Burget-Rimin Keɓe; Nura Sani, mazaunin Rimin Keɓe; Sulaiman Shu’aibu, mazaunin Kwana Hudu; Muhammad Yusuf, mazaunin Na’ibawa; da Sadik Garba, mai shekaru 25, mazaunin Rimin Keɓe.

Kwamandan rundunar ya ce abin mamaki shi ne yadda ɗaya daga cikin waɗanda aka kama ya nuna wa jami’an yadda suke satar wayoyin mutane, inda har ya yi nasarar zare wayar wani jami’i ba tare da ya ankara ba.

A wani rahoto da Dala FM Kano ta ruwaito, Sani Ibrahim, ɗaya daga cikin waɗanda aka kama, ya bayyana cewa suna da tawagogi kusan biyar da ke gudanar da satar wayoyi da kuɗaɗe a yankin Bata da Ƴan Kura.

Ya ce ya shafe kusan shekaru 10 yana aikata satar wayoyi, amma ya bayyana cewa ya yanke shawarar daina wannan aika-aika.

Ya ƙara da cewa ba sa satar wayoyi ko kuɗaɗen ’yan kasuwa da ke cikin tawagarsu saboda sun san juna.

Shi kuwa Abdullahi Naziru Mustapha Yakasai, wanda ya ce an sace masa wayarsa a kasuwar Ƴan Kura, ya bayyana farin cikinsa kan yadda jami’an rundunar suka kama waɗanda ake zargi tare da ƙwato masa wayarsa da mayar masa da ita.

Advertisement

A ƙarshe, rundunar ta gargaɗi masu aikata satar wayoyi da sauran laifuffuka da su daina, tana mai cewa za ta ci gaba da gudanar da samame domin kamo duk waɗanda ke da hannu a irin waɗannan ayyuka.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending