Connect with us

News

Babu Minista Ko Babban Jami’in Gwamnati Da Zai Yi Amfani Da Motoci Fiye Da 3 A Tawagar Sa —Shugaba Tinubu

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da dukkanin ministoci da shugabannin hukumomin ƙasar amfani da motoci sama da guda 3 a jerin gwanonsu.

Wannan ya biyo bayan umarnin da shugaban ya bayar ɗauke da sa hannunsa a yau Alhamis. Kamar yadda mai taimaka masa kan sadarwa Bayo Onanuga ya tabbatar.

Mun Soma Gyara A Tashar Da Ta Haifar Da Katsewar Wutar Lantarki A wasu sassan Najeriya —TCN

A watan Janairu shugaban ya ɗauki matakin rage kashe kuɗi a gwamnati ta hanyar rage adadin waɗanda za su na masa rakiya daga 50 zuwa 20 a tafiye-tafiye na ƙasashen waje sai kuma mutum 25 a tafiye-tafiye na cikin gida.

Shugaban ya kuma umarci a bawa dukkanin ministoci da shugabannin hukumomi jami’an tsaro guda 5 kawai, waɗanda suka haɗar da ƴan sanda 4 da jami’in hukumar farin kaya guda 1.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending