Connect with us

News

Kotu Ta Haramta Wa Gwamna Lucky Aiyedatiwa Neman Wani Wa’adin

Published

on

Lucky Aiyedatiwa

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Akure, Babban Birnin Jihar Ondo, ta yanke hukuncin cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa bai da damar sake tsayawa takarar wani wa’adin mulki a kujerar.

Da yake gabatar da hukuncin a ranar Alhamis, Mai Shari’a Toyin Bolaji Adegoke ya bayyana cewa kundin tsarin dokokin Nijeriya na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima) bai ba wa zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, gwamna ko mataimakin gwamna damar cigaba da riƙe muƙamin ba na tsawon sama da shekaru takwas.

Advertisement

Dakarun Soji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda  20 Ciki Har Da Kwamandan ISWAP A Yobe

Kotun ta yi wannan hukunci ne bayan gabatar da wani ƙorafi a gabanta da ke ƙalubalantar cancantar Aiyedatiwa na sake tsayawa takarar gwamnan jihar.

Advertisement

A ranar 27 ga watan Disambar 2024 ne aka rantsar da Aiyedatiwa a matsayin gwamna a Ondo bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu.

Daga bisani ya tsaya takara kuma ya ci zaɓe wanda aka yi a 16 ga Nuwamban 2024 bayan ya doke Agboola Ajayi na jam’iyyar PDP, inda kuma aka sake rantsar da shi a 24 ga Fabrairun 2025.

Advertisement

Saidai, wani mamban APC mai suna Dakta Akin Ebguwalo, a gaban kotun ya ƙalubalanci cancantar gwamnan na sake neman wani wa’adin.

Akan haka ne kotun ta ce ƙyale Aiyedatiwa ya sake tsayawa takara zai saɓa wa hukuncin dokar ƙasa da ya taƙaice zangon zaɓaɓɓun jami’ai.

Advertisement

 

THE CABLE 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending