Connect with us

News

Muhimman bayanan da jawabin sabon jagoran addini na Iran ya ƙunsa

Published

on

FB IMG 1773013730560

Sabon jagoran addinin kasar Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei, ya bayyana cewa ƙasarsa na buƙatar inganta dangantaka da makwabtanta.

Wannan jawabi nasa shi ne na farko tun bayan rantsar da shi a matsayin jagoran addini na ƙasar, biyo bayan rasuwar mahaifinsa, Ali Khamenei a farkon wannan watan, sai dai Mojtaba bai bayyana a bidiyo ba, kamar yadda aka yi tsammani.

Advertisement

Muhimman bayanan da jawabin sabon jagoran addini na Iran ya ƙunsa

Mojtaba Khamenei, ya jaddada mahimmancin ƙulla dangantaka mai kyau da ƙasashen yankin domin tabbatar da zaman lafiya.

Advertisement

Duk da kiran sulhun da ake yi, Khamenei ya bayyana cewa Iran za ta ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka da ke ƙasashen makwabta muddin ba a rufe su ba.

Ya bayyana cewa Iran za ta ci gaba da amfani da ƙarfin ikon da take da shi na rufe mashigar tekun Hormuz a matsayin makamin kariya ga abokan gaba.

Advertisement

Jagoran ya lura da cewa dakarun ƙasar sun yi aiki tuƙuru wajen kare mutuncin Iran daga hare-haren maƙiya, saboda haka ya yi alkawarin ɗaukar fansar jinin waɗanda aka kashe a yayin fito-na-fito da Amurka da Isra’ila.

Khamenei ya gode wa sojojin ƙasar waɗanda ya ce sun hana a yi wa Iran mamaya ko raba kan ‘yan ƙasar yayin da ake kai mata hari.

Advertisement

“Ina so na gode wa jaruman mayaƙanmu waɗanda ke ci gaba da yin aiki tuƙuru a lokacin da ƙasarmu ke fuskantar matsin lamba daga abokan gaba,” in ji Khamenei.

Wannan mataki na Mojtaba Khamenei ya biyo bayan kalamai makamantan haka daga Shugaba Masoud Pezeshkian, wanda shi ma ya ba wa ƙasashe makwabta hakuri kan hare-haren da suka shafi yankunansu, yana mai cewa babban burin Iran shi ne kawar da duk wasu manufofin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.

Advertisement

 

 

Advertisement

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending