Connect with us

News

Dakarun Sojin Sun Kwato Dabbobi 529 Daga Hannun Barayin Daji A Katsina

Published

on

IMG 20260209 124321 487
Spread the love

Rundunar Sojojin Nijeriya ta ce dakarunta na Forward Operation Base (FOB) Malumfashi da ke aikin wanzar da tsaro a Jihar Katsina sun ƙwato dabbobi 529 daga hannun ɓarayin daji bayan sun yi fafatawa mai zafi da ‘yanta’addan.

‎Wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Lahadi ta ce dakarunta, waɗanda Laftanar Kanar MM Isa, ya jagoranta bayan sun samu bayanan sirri game da ɓarayin dajin, sun yi musu kwanton-ɓauna a yankin Kasuwan Sabo na ƙaramar hukumar Kafur ranar 7 ga watan Fabrairun 2026.

Gwamnan  Abia Ya Sanya Hannu Kan Dokar Tallafin Tsofaffi

‎Ta ƙara da cewa ɓarayin dajin sun shiga Katsina ne daga Jihar Zamfara kuma Idi Abasu Aiki, ɗan’uwan gawutaccen ɗan fashin dajin nan Ado Aliero, shi ne ya shugabance su.

‎Bayan sojojin Nijeriya sun ci ƙarfin ‘yan fashin dajin, sun ƙwato dabbobi 529 da suka haɗa da shanu 290, da tumaki 238 da jaki ɗaya da kuma babur guda ɗaya, in ji sanarwar. Sanarwar ta ce babu wani sojan Nijeriya da ya mutu ko ya jikkata.

 

TRT AFRIKA

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *