News
Jami’an ’Yan Sanda Sun Cafke Matashi Bisa Zargin Garkuwa Da Mahaifinsa
A jihar Adamawa, rundunar ’yan sanda ta cafke wani matashi da ake zargi da hannu a garkuwa da mahaifinsa, a wani lamari da ya janyo cece-kuce a tsakanin al’umma.
Kakakin rundunar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya ce kamen ya biyo bayan wani samame na haɗin gwiwa da jami’an tsaro suka kai maboyar masu garkuwa da mutane da ke ƙauyen Jera, a gundumar Malabu ta ƙaramar hukumar Fufore, bayan samun sahihan bayanan sirri.
Dakarun Soji Sun Hallaka Ƴan Boko Haram 30 Tare Da Ƙwato Mutane 700 Da Aka Yi Garkuwa Da Su
A cewar rundunar, binciken farko ya nuna cewa matashin na daga cikin mutanen da suka sace Alhaji Ahmadu a ranar 30 ga Janairu, 2026. Rahoton ya ƙara da cewa abin mamaki, wanda ake zargin ɗan mutumin da aka sace ne, tare da wasu mutane biyu da suka amsa hannu a aikata laifin.
’Yan sandan sun bayyana cewa ana ci gaba da ƙoƙarin ceto wanda aka sace cikin koshin lafiya, tare da ci gaba da neman sauran waɗanda ake zargi da hannu a lamarin.
Rundunar ta kuma yi kira ga jama’a da su rika bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai, domin taimakawa wajen yaƙi da garkuwa da mutane da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
