News
Jami’an ’Yan Sanda Sun Cafke ’Yan Fashi Biyar A Jigawa
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta cafke ’yan fashi biyar da ake zargi da aikata fashin makami da satar gidaje a wasu sassan jihar, tare da kwato kayayyakin sata daga hannunsu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Shi’isu Adam, ya tabbatar da cafken cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, yana mai cewa nasarar ta biyo bayan tsauraran sintiri da hadin gwiwa tsakanin ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro.
Jami’an ’Yan Sanda Sun Cafke Matashi Bisa Zargin Garkuwa Da Mahaifinsa
A cewarsa, a ranar 6 ga Fabrairu, 2026, wata tawagar sintiri ta cafke Ahmed Musa, mai shekara 22, a karamar hukumar Taura, tare da wayoyin hannu, katunan ATM da kuma kudade da ake zargin kayan sata ne.
SP Adam ya ce binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin na daga cikin wata kungiyar ’yan fashi da ke kai hare-hare da satar gidaje a garin Taura da makwabtansa.
Haka kuma, ’yan sanda daga Sashen Ringim sun cafke sauran ’yan fashi hudu, ciki har da Abdullahi Danladi, mai shekara 20, inda suka kwato na’urorin POS guda biyu, wayoyin hannu, katunan ATM da wasu kayayyaki.
Ya ce dukkan ’yan fashi biyar an mika su zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin ci gaba da bincike da gurfanar da su a gaban kotu.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ya yabawa jami’an da suka gudanar da aikin, yana mai jaddada kudirin rundunar na dakile ayyukan fashi da makami a fadin jihar.
