Connect with us

News

Jirgi Ya Fadi A Teku Dauke Da Fasinjoji Sama Da 50

Published

on

aircraft carrying 50 people shoreline 1057933869
Spread the love

Wani jirgin sama mallakin kamfanin StarSky Airline, dauke da Fasinjoji 55, ya fadi cikin tekun Indiya jim kadan bayan tashinsa daga Filin Jirgin Sama na Aden Adde da ke Mogadishu, babban birnin Somaliya.

‎Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Somaliya (SCAA) ta tabbatar da cewa hadarin ya faru ne sakamakon matsalar fasaha da ta taso bayan tashin jirgin, lamarin da ya hana shi samun isasshen tsayi a sararin samaniya.

Jami’an ’Yan Sanda  Sun Cafke ’Yan Fashi Biyar A Jigawa 

Advertisement

‎Hukumar ta ce dukkan fasinjoji da ma’aikatan jirgin sun tsira , kuma an kwashe su cikin gaggawa zuwa wuraren da suka dace.

‎An rufe filin jirgin na Aden Adde na dan lokaci domin bai wa jami’an agajin gaggawa damar gudanar da aiki, amma daga bisani aka sake bude shi.

Advertisement

 

THE SUN

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *