Connect with us

News

Hatsarin Jirgin Yaƙi Mai Saukar Ungulu Ya Hallaka Dakarun Sojin Koriya Ta Kudu

Published

on

1a6987add4dbae3b741b639ad17f9d5338c5b80f3747871f2aa5043f69c23ef0
Spread the love

Rundunar sojin Koriya ta Kudu ta tabbatar da mutuwar jami’anta biyu sakamakon hatsarin wani jirgin yaƙi mai saukar ungulu kirar AH-1S Cobra da ya faɗi yayin atisaye a safiyar Litinin.

Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya faru ne a garin Gapyeong, da ke arewacin ƙasar, a lokacin da sojojin ke gudanar da atisayen koyon dabarun saukar gaggawa idan aka samu matsala yayin aiki.

Wani Matashi Ya Rasu Yayin Kokarin Ciro Tukunyar Gas Daga Rijiya A Kano ‎

Likitoci sun tabbatar da mutuwar jami’an sojin bayan an garzaya da su asibiti domin ceto rayukansu, lamarin da ya tilasta wa rundunar sojin ƙasar dakatar da duk wasu atisayen jiragen yaƙi masu saukar ungulu irin na AH-1S Cobra har sai an kammala bincike.

A sanarwar da rundunar sojin ta fitar, ta bayyana cewa za a gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin faɗuwar jirgin, tare da ɗaukar matakan da suka dace don kauce wa afkuwar irin wannan hatsari a nan gaba.

Har zuwa lokacin wallafa wannan labari, mahukuntan Koriya ta Kudu ba su bayyana takamaiman abin da ya janyo hatsarin ba.

 

TRT WORLD 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *