Connect with us

Politics

Kimanin Mutum 500 Ne Suka Amfana Da Tallafi A Garko, Kwamishinan Ƙasa Ya Yaba wa Gwamnan Kano kan Ayyukan Ci Gaba‎

Published

on

IMG 20260208 WA0304 768x576
Spread the love

Kimanin mutum 500 ne suka ci gajiyar wani shirin tallafi da Kwamishinan Ƙasa da Tsara Birane na Jihar Kano, Abduljabbar Muhammad Umar, ya ƙaddamar a Ƙaramar Hukumar Garko.

Shirin ya haɗa da rabon babura 100 da kuma tallafin kuɗi ga matasa, shugabannin gundumomi da wasu jiga-jigan siyasa daga mazabu 10 na ƙaramar hukumar, da nufin tallafa wa rayuwar jama’a da bunƙasa tattalin arziƙin yankin.

An Gurbata Harkar Tsaro Da Siyasa A Najeriya  — Lawal Daura

Da yake jawabi a wajen taron, Abduljabbar Muhammad Umar ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ke aiwatarwa a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar.

A cewarsa, ayyukan da suka shafi gyaran hanyoyi, inganta asibitoci, samar da ruwan sha da bunƙasa kasuwanni na taimakawa wajen inganta rayuwar al’umma, musamman a yankunan karkara.

Kwamishinan ya ce shirin tallafin wani ɓangare ne na ƙoƙarinsa na taimaka wa al’ummar Garko tare da tallafa wa manufofin gwamnatin jihar.

A nasa ɓangaren, wakilin Gwamnan Kano, Hamza Buhari Bakwana, ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da goyon bayan ayyukan raya ƙasa tare da haɗin gwiwa da sauran matakan gwamnati.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *