Connect with us

News

Wani Matashi Ya Rasu Yayin Kokarin Ciro Tukunyar Gas Daga Rijiya A Kano ‎

Published

on

images (4)
Spread the love

Wani matashi ɗan kimanin shekara 30 ya rasa ransa a ƙaramar hukumar Gwarzo ta jihar Kano, yayin da yake ƙoƙarin ciro Tukunyar Gas da ke ci da wuta daga cikin wata rijiya.

‎Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Saminu Abdullahi, ya fitar a ranar Litinin.

Dakarun Sojin Sun Kwato Dabbobi 529 Daga Hannun Barayin Daji A Katsina

‎A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne da yammacin Lahadi a Unguwar Saulawa da ke cikin garin Gwarzo, inda reshen hukumar kashe gobara na yankin ya samu kiran gaggawa daga wani mazaunin unguwar, Alhaji Dan Gwarzo.

‎Sanarwar ta bayyana cewa mamacin, mai suna Ashahabu Ubale, ya shiga rijiyar ne domin ƙoƙarin ciro tankar gas da aka jefa ciki tana ci da wuta. Sai dai yayin da yake cikin rijiyar, tankar gas ɗin ta buɗe tare da sakin iskar gas mai yawa, lamarin da ya rage iskar oxygen a cikin rijiyar, wanda hakan ya janyo masa shakewa.

‎Jami’an kashe gobara sun samu nasarar fitar da matashin daga rijiyar a sume, tare da garzaya da shi asibiti domin samun kulawar gaggawa.

‎Amma daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

‎A halin da ake ciki, hukumar ta kuma bayyana damuwarta kan yawaitar hatsarurrukan nutsewa da ake samu a jihar. A baya-bayan nan, wani matashi ɗan shekara 18, Yusif Malam-Gwani, ya nutse a wani tafkin ruwa da ke Bachirawa, Kwanar Madugu, a ƙaramar hukumar Ungogo.

‎Haka kuma, wani yaro ɗan shekara takwas, Abdussalam Ibrahim, ya rasa ransa bayan da ya faɗa cikin wata rijiya a Kofar Yamma, garin Karaye, da ke ƙaramar hukumar Karaye.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *