News
Himma Radio Ta Mayar Da Yara 80 Makaranta A Kano
An wani mataki na taimakawa alumma tashar Himma Radio dake Kano ta dauki nauyin mayar da Yaran da basa zuwa makaranata 80 a Karamar Hukumar Madobi.
Da yake jawabi Hakimin Madobi Sale Musa Sale Kwankwaso ya dau ki alkawarin mayar da Yara kimanin guda dari shida (600) makaranta domin rage yawan yaran da basa zuwa makaranata a Karamar Hukumar.
Shugaban NAHCON Sheikh Abdallah Saleh Pakistan Ya Yi Murabusl
Alhaji Musa Sale ya yace a madadinsa da sauran masu rike da masarautun gargajiya zamu dauki nauyin mayar da yara 50 a dukkan mazabu goma sha biyu dake wannan Karamar Hukumar.
Da yake Jawabi Shugaban Karamar Hukumar Madobi Sulaiman Dan Azumi wanada ya samu wakilcin kakakin majalisar Karamar Hukumar kansilan mazabar Kafin Agur, Hon. Tijjani Rabi’u Kafi, ya tabbatar da bayar da gudunmar karamar Hukumar wajen cigaban Ilimi domin cigaban alumma.
Da yake karin haske akan dalilin shirya taron da tashar Himma Radio ke cigaba da yi na daukar nauyin mayar da Yaran makaranata shugaban tashar Alhaji Isma’il Yusuf Makwarari yace hakan yana daga cikin wani shiri na hidimtawa alumma da tashar ta assasa don bayar da gudunmawa wajen cigaban alumma.
Sanan ya bada shawarar kaddamar da awasusun tallafawa Ilimi a Karamar Hukumar wato “Madobi Education Trust Funds”
A Jawabinsa Sakataran Ilimi na Karamar Hukumar Madobi Lawan Sani Gora kira ya yi ga iyayen yaran kan su sanaya idanu kan tabbatar da cewar yaran suna zuwa makaranata don samun nasarar shirin.
Akarshe Hakimin Madobi ya amunce da kafa Asusun tallafawa Ilimi a Karamar Hukumar tare da bayar da watanni uku don kaddamar da shirin.
Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki akan harkokin ilimi, da masu rike da masarautun gargajiya na Karamar Hukumar ta Madobi.
