News
GIOPPINI Ta Yi Karin Haske Kan Rahoton Kananan Yara Masu Gararamba A Titunan Kano
Babban Daraktan Global Improvement of Less Privileged Persons Initiative (GIOPPINI), Mohammed Ali Mashi, ya ce rahoton da aka fitar kan yawan Kananan Yara Masu Gararamba A Titunan Kano ba shi da nufin bata sunan gwamnati ko haifar da sabani.
A cewarsa, kalaman da ya yi sun kasance ne domin jawo hankalin mahukunta kan matsalolin da ke bukatar kulawa, musamman halin da wasu yara marasa galihu ke ciki.
Rigakafin Cutar Shanu Na Kara Karfi A Kano, Kumbotso Ta Shiga Zagaye Na Biyu
Mashi ya bayyana cewa wasu daga cikin yaran na kwana a karkashin gada ko yawo a tituna da dare, lamarin da ke jefa su cikin hadarin kamuwa da cututtuka da sauran matsalolin lafiya. Ya ce damuwarsa da ta kungiyarsa ta samo asali ne daga burin inganta rayuwar yara masu rauni da kuma tallafa wa kokarin gwamnati wajen magance matsalolin zamantakewa.
Ya kuma jaddada cewa kungiyarsu na goyon bayan kokarin gwamnati, tare da cewa ba su da niyyar gabatar da kididdiga ko bayanan da ba su da tushe.
Sai dai tun bayan wallafar rahoton a wasu kafafen sadarwa, Kano State Bureau of Statistics ta yi watsi da ikirarin, tana mai cewa ya saba da sahihan bayanan da take da su.
A wata sanarwa da Suraj Sulaiman, Darakta Janar na hukumar, ya sanya wa hannu, an ce rahoton da aka danganta da GIOPPINI na cewa sama da yara ‘yan titi miliyan biyu na kwana a wurare marasa tsabta da tsaro ba ya dace da bayanan kididdigar hukuma.
