News
Inna Lillahi Wa Inna Ilaihirrajiun Allah Ya Yiwa Hajiya Lami Hafsat Maccido Rasuwa
DAGA SUNUSI K/NAISA
Fitacciyar kuma ƙwararriyar mai karanta labarai, Hajiya Lami Hafsat Maccido, ta rasu tana da shekaru 72 bayan gajeriyar rashin lafiya.
Rahotanni sun nuna cewa ta rasu ne a daren Talata, lamarin da ya jefa al’ummar kafafen yaɗa labarai, musamman a Arewacin Nijeriya, cikin jimami. Injiniya Abubakar Garba Maccido ne ya sanar da rasuwar ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin WhatsApp.
GIOPPINI Ta Yi Karin Haske Kan Rahoton Kananan Yara Masu Gararamba A Titunan Kano
Marigayiyar ta yi fice a tarihin aikin yaɗa labarai, kasancewarta mace ta farko ‘yar asalin Nijeriya da ta fara gabatar da shirye-shirye a Radiyon Kano, sannan tana daga cikin mutanen farko da suka bayyana a allon talabijin na NTA Kano da CTV 67 tun farkon kafuwarsu.
Masana da abokan aikinta na kallon rasuwarta a matsayin babban rashi ga fannin yaɗa labarai, inda muryarta da ƙwarewarta suka taimaka wajen gina tubalin shirye-shiryen radiyo da talabijin na zamani a Kano da ma Arewacin ƙasar baki ɗaya.
An haifi Hajiya Lami Maccido a ranar 12 ga Agusta, 1954 a Jos, Jihar Filato. Mahaifinta ɗan asalin Jihar Borno ne, yayin da mahaifiyarta Bafulatana ce daga Jihar Katsina.
Ta yi karatun firamare a Township Primary School, sannan ta halarci St. Louis Secondary School, duk a Jos. Daga nan ta ci gaba da karatun gaba da sakandare a ABC/ABU Kano.
Ta fara aiki a matsayin mai karɓar kuɗi a Sheshe Departmental Stores da ke Kano, kafin daga bisani ta shiga Radiyon Kano a shekarar 1974, inda ta yi aiki har zuwa 1976.
Daga nan ta koma NTA Kano (wadda a lokacin ake kira NTV Kano), inda ta yi aiki daga 1976 zuwa 1981. Bayan haka ta shiga CTV 67 a matsayin ɗaya daga cikin ma’aikatan farko na tashar.
Ta yi ritaya a shekarar 2012 bayan shafe kusan shekaru 35 tana hidima cikin sadaukarwa a harkar yaɗa labarai.
Marigayiyar, tare da wasu manyan abokan aikinta, sun taka muhimmiyar rawa wajen sanya sunan CTV 67 (Community Television) a lokacin da aka kafa tashar a zamanin tsohon gwamnan Jihar Kano, Abubakar Rimi.
Rasuwarta ta jawo ɗimbin saƙonnin ta’aziyya daga ‘yan jarida, tsoffin abokan aiki da masoya, inda da dama suka bayyana ta a matsayin jagora mai daraja, ƙwararriyar ma’aikaciya, kuma abar koyi ga sabbin masu shiga harkar yaɗa labarai.
Masu ta’aziyya sun ce sadaukarwa, ƙwarewa da nagartarta za su ci gaba da kasancewa abin tunawa a tarihin aikin yaɗa labarai a Nijeriya.
