News
DSSS Ta Sake Kama El-Rufai Bayan EFCC Ta Ba Shi Beli
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta Ƙasa (DSS) ta sake kama tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a daren Laraba, jim kaɗan bayan Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta bayar da belinsa.
Rahotanni sun ce EFCC ta tsare El-Rufai tun ranar Litinin kan zarge-zargen almundahana. Sai dai da misalin ƙarfe 8 na dare aka ba shi beli, inda jami’an DSS suka karɓe shi a harabar hedikwatar EFCC.
Inna Lillahi Wa Inna Ilaihirrajiun Allah Ya Yiwa Hajiya Lami Hafsat Maccido Rasuwa
Ana danganta sabon kamen da zargin aikata laifukan yanar gizo, musamman zargin katsalandan da kuma satar sauraron tattaunawar wayar Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu.
Tun a ranar Litinin ne DSS ta gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin karya dokar Cybercrimes (Amendment) Act, 2024 da kuma Nigerian Communications Act, 2003. Har yanzu ba a sanya ranar fara shari’a ba, kuma El-Rufai bai fito da martani kai tsaye kan tuhume-tuhumen ba.
Lamarin ya biyo bayan takaddama da ta taso a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, inda aka ce an yi yunƙurin kama shi bayan dawowarsa daga ƙasar Masar. El-Rufai ya zargi NSA da bayar da umarnin kama shi, zargin da ya fito fili a wata hira da ya yi a gidan talabijin.
Lauyansa, Ubong Akpan, ya soki matakin, yana mai cewa an take masa haƙƙin ɗan ƙasa, musamman dangane da ƙwace fasfo ɗinsa.
El-Rufai, wanda ya rike gwamnan Kaduna daga 2015 zuwa 2023, ya shiga jam’iyyar ADC, kuma ya zama ɗaya daga cikin masu sukar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ana sa ran ci gaban shari’ar zai ƙara fito da bayanai kan tuhume-tuhumen da ake masa.
