News
Shugaba Tinubu ya sa hannu kan sabuwar dokar zaɓe
Shugab Bola Tinubu ya sanya hannu akan dokar zaɓen Nijeriya ta 2022 da aka yi wa gyaran fuska, jiya Laraba.
Hakan na zuwa ne kwana ɗaya bayan Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince da dokar bayan kwashe watanni ana tafka muhawara akanta.
DSSS Ta Sake Kama El-Rufai Bayan EFCC Ta Ba Shi Beli
Gyaran dokar ya haifar da zazzafar muhawara a makon da ya gabata bayan wasu al’ummar ƙasar da kuma ‘yan majalisa na jam’iyyar adawa suka nuna ƙin amincewa da ɓangaren dokar da ya yi magana akan tura sakamakon zaɓe.
An riƙa taƙaddama akan matsayar da majalisar ta ɗauka na cewa za a iya amfani da takardar tura sakamakon zaɓe idan aka samu tangarɗar tura sakamakon ta na’ura.
A ranar Talata majalisar dattijai ta sanya hannu kan dokar duk da hargitsi da aka samu a zauren majalisar yayin karatu akan dokar..
