Connect with us

News

Falalar Goman Farko Ta Azumin Ramadan

Published

on

images (2)

Musulmai a faɗin duniya sun fara gudanar da azumin watan Ramadana, ɗaya daga cikin ginshiƙan addinin Musulunci.

A Najeriya da Saudiyya da ma ƙasashe da dama na duniya an tashi da azumin ne a ranar Laraba 18 ga watan Fabarairu bayan ganin jinjirin wata.

Advertisement

Musulmai za su kwashe tsawon kwana 29 ko 30 suna gudanar da azumin na Ramadana.

Kamar kowace ibada a Musulunci, azumin watan Ramadana na da falala sosai, inda Musulmai ke mayar da hankali wajen neman yardar Allah.

Advertisement

Sai dai malamai na cewa akwai wasu ibadu na musamman da suka keɓanta da kwanaki goma-goma na wannan wata mafi tsarki a kalandar Musulmai.

An bayyana cewa kwanakin watan na farko sun kasance na samun rahama, tsakiyar watan kuma lokaci ne na samun yafiya sai kuma ƙarshen watan wanda kan zama lokacin samun ƴanci daga azaba.

Advertisement

Wannan maƙala ta nemi ji daga bakin masana addinin game da falalar da ke tattare da goman farko na watan.

 

Advertisement

Ɗaura ɗamara

Ganin cewa azumi ibada ce da ke ɗaukar tsawon lokaci na kwana 29 ko 30, akwai buƙatar jikin ɗan’adam ya ɗan ɗauki lokaci kafin ya saba da ita.

Advertisement

Ma’ana, goman farko ta watan za ta kasance kamar sharar fage na abubuwan da mutum zai gudanar a sauran kwanakin.

Anas Salisu malami ne a birnin Kano na arewacin Najeriya, kuma ya shaida wa BBC cewa magabata ba su cika alaƙanta wata takamaimiyar ibada ba da goman farko ta Ramadana.

Advertisement

“Ba a samu wata keɓantacciyar ibada da aka ruwaito daga Annabi (SAW) ba da aka ce yana yin ta a goman farko na azumin Ramadana kaɗai,” kamar yadda malamin ya yi bayani.

“Sai dai, an samu cewa yana yin ibadu kamar sallar Tarawihi, da sallar tsakar dare, da karatun Ƙur’ani da sauransu.”

Advertisement

Sai dai malamin ya ce babu laifi idan Musulmi ya ɗauki goman farkon a matsayin mafarin wata gagarumar ibada.

“Mutum zai iya horar da kansa ta hanyar bi a hankali, ya zama kowacce rana yana ƙara yawan ibadar da zai riƙa yi, kamar yadda aka samu Annabi (S.A.W) yana yi a goman farko da ta biyu.

Advertisement

“Idan goman ƙarshe ta shigo, hadisai sun tabbatar da cewa Annabi ba ya barci saɓanin sauran kwanakin.”

Shi ma Sheikh Abdussalam Abubakar Baban Gwale a Kanon ya ce salon ibadar da Annabi Muhammadu (SAW) ke yi a goman farko da ta biyu ya sha bamban da sauran.

Advertisement

“Wani hadisi na Nana Aisha Allah ya ƙara yarda a gare ta, ya nuna cewa a goman farko da ta biyu Annabi kan yi barci a wani ɓangare na dare sannan ya raya wani ɓangaren da ibadu,” a cewar malamin.

A gefe guda kuma, Malam Abdulwahhab Harun a jihar Kaduna ya ce yana da kyau mutum ya kula da taƙawa a farkon azumi.

Advertisement

“Misali, ya kamata mutum ya fara zuwa masallaci domin gudanar da sallar Tarawihi tun daga daren da aka ga watan azumi saboda shi ne daren farko na Ramadana,” in ji shi.

“Haka nan, yana da kyau mutum ya koyi tausayi, da haƙauri a goman farko. Tun da wanda bai koyi waɗannan abubuwan ba a goman farko yana da wuya ya iya yinsu a sauran kwanakin.

Advertisement

 

 

Advertisement

BBC HAUSA 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending