News
Gwamnatin Kano Ta Sanar Da Ranakun Komawa Makaranta
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana ranar Lahadi ranar Lahadi, 22 ga watan Maris 2026, a matsayin ranar komawa makaranta ga ɗaliban makarantun kwana na gwamnati da masu zaman kansu, a matakin firamare da sakandare, domin cigaba da zangon karatu na biyu na shekarar 2025/2026.
Yayin da ɗalibai a makarantun jeka Ka dawo a faɗin jihar za su koma makaranta a ranar Litinin 23 ga Maris, 2026.
RANAR RUWA TA DUNIYA: Shin Yaushe Dokar Ta Bacin Gwamnatin Kano Zata Fara Aiki?
A cikin wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta jihar, Musbahu Aminu Yakasai ya fitar, ya bukaci iyaye da masu kula da ɗalibai da su lura da ranar komawar makaranta domin tabbatar da bin wannan umarni gaba ɗaya.
Sanarwar ta ambato Kwamishinan Ilimi, Dr. Ali Haruna Makoda, yana jaddada cewa za a ɗauki matakin ladabtarwa ga duk wani ɗalibi ko ɗaliba da ya ƙi bin wannan umarni.
Ya shawarci ɗalibai da su guji kawo haramtattun abubuwa irin su wuka, reza ko miyagun ƙwayoyi zuwa makaranta, tare da zama masu bin doka domin samun nasara a karatunsu.
