News
Kotu Ta Daure Tsohon Mukaddashin Akanta-Janar Na Tarayya Shekaru 72 A Gidan Yari
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa tsohon mukaddashin Akanta-Janar na Tarayya, Chukwunyere Nwabuoku, hukuncin ɗaurin shekaru 72 a gidan ajiya da gyaran hali bisa samunsa da laifin karkatar da kuɗaɗe har Naira miliyan 868.
Alƙalin kotun, Mai shari’a James Omotosho, ya yanke hukuncin ne a ranar Litinin, bayan ya same shi da laifi a dukkan tuhume-tuhume tara da Hukumar EFCC ta gabatar a kansa, waɗanda suka shafi halasta kuɗaɗen haram.
Yan Najeriya Na Fuskantar Kuncin Rayuwa Yayin Da Farashin Fetur Ya Kai N1,400
Kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru takwas kan kowace tuhuma, wanda ya kai jimillar shekaru 72. Sai dai alkalin ya umarci cewa a aiwatar da hukuncin a lokaci guda, wanda ke nufin zai yi zaman shekaru takwas ne kacal.
Alƙalin ya bayyana laifin a matsayin abin takaici, musamman ganin cewa kuɗaɗen da aka karkatar an ware su ne domin harkokin tsaro da sojoji.
Haka kuma, kotun ta lura cewa wanda aka yankewa hukuncin ya mayar da wani ɓangare na kuɗaɗen da aka karkatar, fiye da Naira miliyan 200, a yayin bincike.
Ana zargin Nwabuoku da aikata laifukan ne a lokacin da yake rike da mukamin Daraktan Kuɗi da Asusun Ma’aikatar Tsaro tsakanin shekarun 2019 zuwa 2021.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
