News
Yan Najeriya Na Fuskantar Kuncin Rayuwa Yayin Da Farashin Fetur Ya Kai N1,400
Farashin man fetur a Najeriya ya ƙara tashi, inda a wasu yankuna ya kai kusan N1,400 duk lita, lamarin da ke ƙara tsananta wahalhalun rayuwar jama’a.
Rahotanni sun nuna cewa tashin farashin man fetur a kasuwar duniya ne ya jawo wannan lamari, wanda ya haddasa tsadar sufuri da rayuwa gaba ɗaya.
BUK Ta Kori Dalibai 171 Kan Takardun Shaidar Shiga Na Bogi
A manyan birane kamar Legas, Kano da Abuja, direbobin haya sun ce ribarsu ta ragu, yayin da fasinjoji ke ƙara raguwa saboda tsadar kuɗin mota kamar yanda Jaridar Aminiya ta ruwaito
A Kano, farashin ya kai har N1,390, inda wasu mazauna suka ce ana karɓar har N4,000 kan tafiyar da a baya ba ta wuce N1,000 ba.
A yankin Kudu kamar Fatakwal da Yenagoa, farashin ya kai N1,800, yayin da farashin sufuri ya ninka sau biyu a wasu wurare.
Manazarta sun yi gargaɗin cewa idan farashin ya ci gaba da hawa, mutane da dama za su daina amfani da motoci, yayin da harkokin kasuwanci ke ci gaba da fuskantar matsin lamba.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
