News
Jami’an Hisbah Sun kama mata sama da 280 Da Su Ka Yi Shigar Banza A Bukukuwan Sallah A Kano
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa ta cafke mata sama da 280 da ake zargi da yin shigar da ba ta dace ba a yayin bukukuwan Sallah da aka gudanar a sassa daban-daban na jihar.
A cewar wata sanarwa da mataimakin babban kwamandan hukumar, Sheikh Mujahideen Aminudeen ya aikewa da Jaridar Inda Ranka, an gudanar da kamen ne ne sakamakon sintiri da jami’an hukumar suka yi a lokacin bukukuwan.
Sanarwar ta kuma ce hukumar ta cafke kusan mata 80 da aka samu suna hawa gefen baburan Adaidaita Sahu, abin da ta bayyana a matsayin karya dokokin amfani da hanya tare da nuna rashin ladabi a fili.
Hisbah ta ce matakan na cikin kokarin tabbatar da tsafta, ladabi da bin ka’idojin zamantakewa, musamman a lokutan bukukuwa, tare da gargadin jama’a da su kiyaye dokoki domin kauce wa hukunci.
Hukumar ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da gudanar da sintiri da sa ido a fadin jihar domin tabbatar da zaman lafiya da kyawawan dabi’u a tsakanin al’umma.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
