Connect with us

News

‎RANAR RUWA TA DUNIYA: Shin Yaushe Dokar Ta Bacin Gwamnatin Kano Zata Fara Aiki? ‎

Published

on

Yan ga ruwa
Advertisements
Advertisements
Spread the love

‎Ranar 22 ga watan Maris ta kowacce shekara rana ce da a kan yi bikin Ranar Ruwa ta Duniya da nufin wayar da kan al’umma game da muhimmancin amfani da tsaftataccen ruwan sha.

‎A kowace shekara dai masu wannan bikin kan yi nazari kan matsalar ruwa yayin da masana ke gargadin cewa samar da wadataccen ruwan sha mai inganci na ci gaba da zama babban ƙalubale a ƙasashe masu tasowa.

Matatar Dangote  Ta Ƙara Farashin Man Fetur Zuwa N1,245 Kan Kowace Lita

Advertisement

 

Matsalar ruwa na ƙara tsananta a Kano

A Jihar Kano, matsalar ƙarancin ruwa na ci gaba da damun al’umma, musamman a lokacin zafi, inda jama’a ke shan wahala wajen samun ruwan sha da na amfanin yau da kullum.

Advertisement

Rahotanni sun nuna cewa matsalar ta fi shafar mazauna ƙananan hukumomi takwas na cikin birnin Kano, da suka haɗa da Dala, Fagge, Gwale, Kano Municipal, Kumbotso, Tarauni, Nassarawa da Ungogo.

Mazauna waɗannan yankuna na dogaro da hanyoyi daban-daban domin samun ruwa, ciki har da rijiyoyin burtsatse, samarwar gwamnati, da kuma sayen ruwa daga masu sana’ar sayar da shi.

A yankunan karkara kuwa, matsalar ta fi tsanani, inda wasu al’umma ke amfani da ruwa mara tsafta, har ma a wasu lokuta suna raba ruwa guda da dabbobi—abin da ke ƙara haɗarin kamuwa da cututtuka.

Advertisement

Bincike ya nuna cewa matsalar na da alaƙa da rashin isasshen wutar lantarki, wanda ke hana tashoshin ruwa aiki yadda ya kamata. Haka kuma, lalacewar kayayyakin aiki da rashin ingantaccen tsarin kula da su na daga cikin dalilan da ke ƙara ta’azzara matsalar.

 

Dokar ta-ɓaci Kano?

Advertisement

A ƙoƙarinsa na magance matsalar, gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ayyana dokar ta-ɓaci a ɓangaren samar da ruwa.

Sai dai watanni bayan sanarwar, har yanzu ba a ga gagarumin sauyi ba, lamarin da ya sa jama’a ke tambayar ko dokar za ta wuce matakin takarda zuwa aiwatarwa.

Masu ruwa da tsaki sun buƙaci gwamnati da ta hanzarta aiwatar da matakan da suka dace domin kawo ƙarshen matsalar.

Advertisement

Sun ce ya zama dole a tabbatar da cewa dokar ta-ɓaci ta haifar da sauyi a zahiri, domin rage wahalar da al’ummar jihar ke fuskanta.

A daidai lokacin da ake bikin Ranar Ruwa ta Duniya, ana sa ran hukumomi za su ɗauki matakan da za su tabbatar da samar da tsaftataccen ruwan sha ga kowa cikin sauƙi da inganci.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending