News
Sheikh Abduljabbar Ya Nemi Kotu Ta Dawo Da Shi Kano Daga Gidan Yarin Kuje
Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara, wanda aka yanke wa hukuncin kisa kan batanci ga Manzon Allah (SAW), ya shigar da sabon korafi yana neman a dauke shi daga Gidan Yarin Kuje da ke Abuja a mayar da shi gidan yarin Kurmawa da ke Kano.
A cikin takardar korafi da aka shigar gaban Kotun Daukaka Kara, reshen Jihar Kano, mai dauke da kwanan wata 3 ga Afrilu, 2026, Abduljabbar Kabara ya ce tsare shi Abuja ya hana shi samun muhimman takardun shari’a da yake bukata wajen daukaka kara.
Gwamnatin Tinubu Ta Shirya Kashe Naira Biliyan 135 Domin Shari’un Bayan Zabe
Ya bayyana cewa takardun, wadanda suka haura shafuka 5,000 na bayanan shari’a da hujjoji, an bar su a Gidan Yarin Kurmawa tun lokacin da aka dauke shi ranar 14 ga Oktoba, 2025.
“Dole ne na tabbatar da cewa takarduna da ke Kurmawa sun cika kuma na asali ne kafin a sake fitar da sanarwar zaman shari’a,” in ji shi a cikin korafin.
Abduljabbar ya nemi kotu ta ba shi kariya uku: dawo da shi Gidan yarin Kurmawa domin tabbatar da takardunsa, dawo da duk wani daftari da aka rasa ko aka sauya, da kuma dakatar da sanarwar zaman shari’a har sai an tabbatar da takardun sun cika.
Malamin, wanda ya nace zai kare kansa da kansa a daukaka kara, ya jingina bukatarsa da Sashe na 36 na Kundin Tsarin Mulki na 1999.
Ya kuma koka cewa duk da ziyarar da magoya bayansa ke yi a kotu, ba a taba fitar da umarnin kawo shi domin halartar zaman karbar daukaka kararsa ba.
Kotun Daukaka Kara dai har yanzu ba ta saka rana don sauraron wannan bukata ba.
Abdulajabbar Kabara na tsare tun daga 16 ga Yuli, 2021 lokacin da aka fara gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Shari’a ta Kofar Kudu da ke Kano kan tuhumar batanci guda hudu ga Annabi Muhammad (SAW).
Kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a Ibrahim Sarki-Yola, ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar 15 ga Disamba, 2022 bayan ta same shi da laifin dukkan tuhumar da Gwamnatin Jihar Kano ta shigar.
