News
Gwamnatin Tinubu Ta Shirya Kashe Naira Biliyan 135 Domin Shari’un Bayan Zabe
Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ware naira biliyan 135.22 domin shari’un zaɓe da abubuwan da ke biyo bayansu a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026, matakin da ya haifar da muhawara mai zafi daga jam’iyyun adawa da masana.
Bayanai sun nuna cewa an bayyana wannan tanadi ne a cikin takardar Majalisar Wakilai mai kwanan watan 31 ga Maris 2026, wadda ke ɗauke da rahoton dokar kasafin kuɗi da ake duba wa a majalisar.
Gwamnatin Zamfara Ta Haramta “Signing Out” Da Ɗalibai Ke Yi A Makarantu
A cewar takardar kasafin, an sanya kuɗin ne a ƙarƙashin Service-Wide Votes, wani asusu na musamman da gwamnatin tarayya ke amfani da shi wajen biyan kuɗaɗen da ba a ware wa wata ma’aikata ko hukuma kai tsaye ba.
Masana sun ce ware irin wannan makudan kuɗi domin shari’un zaɓe na iya nuna cewa gwamnati na hasashen yawaitar ƙalubalantar sakamakon zaɓe a kotuna bayan zaɓen 2027.
A watan Fabrairu 2026, INEC ta sanar da Majalisar Tarayya cewa tana buƙatar naira biliyan 873.78 domin gudanar da zaɓen 2027. Haka kuma ta nemi ƙarin naira biliyan 171 domin ayyukanta na shekarar 2026.
Sai dai masu sharhi sun lura cewa wannan tanadi na N135.22bn domin shari’un zaɓe bai fito fili ba a farkon daftarin kasafin da aka gabatar, abin da ya ƙara janyo tambayoyi kan yadda aka ƙara shi daga baya.
Jam’iyyun adawa, musamman PDP da ADC, sun soki wannan mataki, suna mai cewa yana tayar da tambayoyi kan gaskiya da dalilin ware irin wannan makudan kuɗi.
Sakataren yaɗa labarai na PDP, Ini Ememobong, ya bayyana cewa tanadin na iya jefa shakku kan sahihancin tsarin zaɓe, yayin da takwaransa na ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce hakan na iya nuna hasashen rikice-rikicen shari’a bayan zaɓe tun kafin a gudanar da shi.
Yayin da Majalisar Tarayya ke ci gaba da nazari kan kasafin kuɗin 2026, wannan batu na ci gaba da ɗaukar hankalin jama’a, inda masana ke cewa yadda za a fayyace wannan tanadi zai taka muhimmiyar rawa wajen gina amincewa da tsarin zaɓe gabanin zaɓen 2027.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
