News
Wasu Mutane Daga Borno Sun Faɗa Wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Shirin Kashe Domin Na Gaje Shi A Mulki” — Shettima
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa wasu mutane daga Jihar Borno sun taɓa kai wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, rahoton ƙarya cewa yana shirin kawar da shi domin ya karɓi mulki.
Shettima ya bayyana hakan ne a yayin jawabin da ya gabatar a wajen bikin ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon Shugaban Ƙasa na mulkin soja, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), mai taken “My Life of Duty and Allegiance,” da aka gudanar a Abuja ranar Talata.
Kanawa Sun Yarda Da Tsarin NDC Kwankwasiyya’ — Hon. Sagir Wada Sinkin
A cewarsa, lamarin ya faru ne a farkon watanni uku bayan hawansu mulki, inda wasu mutane suka yi ƙoƙarin haifar da rashin fahimta tsakanin sa da Shugaban Ƙasa ta hanyar yaɗa jita-jitar cewa yana da mugun nufi na neman karɓe mulki ta hanyar tashin hankali.
Shettima ya ce waɗannan zarge-zarge ba su da tushe, yana mai jaddada cewa dangantakarsa da Shugaba Tinubu ta kasance mai ƙarfi da kuma haɗin kai wajen tafiyar da gwamnati.
Ya ƙara da cewa irin waɗannan jita-jita na siyasa kan iya haifar da rarrabuwar kai idan ba a yi taka-tsantsan da su ba, musamman a lokacin farkon sabuwar gwamnati.
