Connect with us

Labarai

Wasu Ɓatagari Sun Ƙwaƙule Wa Yarinya Mai Shekara 5 Idanu A Kano

Published

on

Hukumomi a Najeriya sun tsaurara matakan tsaro da kuma sa ido sosai a birnin Kano,
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

An gano gawar wata yarinya mai shekaru biyar, Humaira Isyaku Umar, a cikin wani kango da ke unguwar Hamza, Rimin Zakara, Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano, bayan ta ɓace tsawon kwanaki uku.

Ana zargin wasu ɓata gari sun ƙwaƙule idanun yarinyar kafin mutuwarta, lamarin da ya janyo damuwa da firgici a tsakanin mazauna yankin.

An Hallaka Wani Ma’aikacin Wutar Lantarki Kan Yanke Wa Wani Gida Wuta

Rahotanni sun ce wasu yara da ke wasa a yankin ne suka gano gawar Humaira a cikin kangon, inda suka lura da cewa an ƙwaƙule mata idanun.

Ƴan uwan mahaifin yarinyar, Hon. Umar Adamu Zakara da Junaidu Abdulkareem Medice, sun tabbatar da gano gawar tare da bayyana yadda aka gano ta, kamar yadda Arewa Updates ta rawaito.

Sai dai har yanzu ba a san waɗanda ake zargin sun aikata laifin ba, yayin da kuma ba a bayyana musabbabin mutuwar yarinyar ba.

Advertisement

Shugaban Kwamitin Ci Gaban Garin Rimin Zakara, Alhaji Baba Habu Mika’ilu, ya ce al’umma ta shirya haɗa kai da jami’an tsaro da matasan yankin domin ƙarfafa sa ido kan mutanen da ba a san su ba da ke shigowa garin.

Ya ce shirin zai taimaka wajen inganta tsaro da kuma hana sake faruwar irin wannan mummunan al’amari.

Rahotanni sun kuma bayyana cewa jami’an ’yan sanda daga ofishin Rijiyar Zaki sun kai ziyara wurin da aka gano gawar yarinyar.

Sai dai ba a bayyana cikakken sakamakon binciken ’yan sanda kan lamarin ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending