Connect with us

News

Kwastam ta kama harsasan da kudinsu ya kai Naira miliyan 557 da aka ɓoye a cikin buhunan Garin kwaki

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar hana fasa kwauri ta kasa (NCS) reshen jihar Ogun ta ce ta kama harsasai 940 da kudinsu ya kai Naira miliyan 557 da aka boye a cikin buhunan garin kwaki Idiroko.

Advertisement

Shugaban yankin, Ahmadu Shuaibu ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a ranar Juma’a a Idiroko, Ogun.

Abu biyar da ake tunanin na karya azumi amma ba sa karyawa —Sheikh Jabir Sani MaiHula

Shuaibu ya ce yayin da suke gudanar da aikin yaki da fasa kwauri a ranar 14 ga watan Maris, jami’an rundunar sun kama wasu harsasai 940 da aka boye a cikin buhunan Garin kwaki.

Advertisement

Ya bayyana cewa, rundunar ta shafe sama da makonni biyu tana bin sahun su tun daga jamhuriyar Benin.

Premium Times ta ruwaito cewa ba a iya kama waɗanda ke ɗauke da waɗannan kaya ba saboda sun arce ne suka bar buhunan garin.

Advertisement

Bugu da kari, hukumar ta ce ta kama buhu 123 da kulli 3,172 na ganyen Wiwi, fatun jakuna 380; Belin kayan gwanjo 304 da kwalaye 910 na Kaji.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending