News
‘Yan Bindiga Sun Harbi Uba Da Ɗansa Tare Da Kwashe Dabbobi Masu Yawa A Katsina
Wasu ‘yan bindiga sun kai mummunan hari kauyen Hayin Kwanta da ke gundumar Sukuntuni a karamar hukumar Kankia ta jihar Katsina, inda suka harbi uba da dansa tare da kwashe dabbobi masu yawa.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kutsa cikin kauyen ne a daren Lahadi kan babura dauke da muggan makamai, inda suka rika harbe-harbe domin tayar da hankalin al’umma.
2026: JAMB Ta Aiyana Maki 150 Mafi Karanci Maki Na Shiga Jami’a A Najeriya
Mazauna yankin sun ce harin ya haddasa firgici matuka, lamarin da ya tilasta wa mutane da dama tserewa zuwa cikin dazuka domin tsira da rayukansu daga hannun maharan.
Majiyoyi daga yankin sun bayyana sunan wadanda suka samu raunukan harbin bindiga da Abashe da dansa, wadanda suka jikkata yayin kokarin guduwa daga maharan.
An ce daga bisani an garzaya da su zuwa wani asibiti a birnin Katsina domin samun kulawar likitoci, inda ake ci gaba da duba lafiyarsu.
Shaidu sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun shafe lokaci suna cin karensu babu babbaka a kauyen ba tare da wata turjiya daga jami’an tsaro ba, duk da kiraye-kirayen neman dauki da mazauna yankin suka yi.
Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, DSP Sadiq Aliyu, ya tabbatar da cewa jami’an tsaro tare da hadin gwiwar sauran hukumomi suna farautar wadanda suka kai harin domin cafke su tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
