News
Shugaban Karamar Hukuma Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Jigawa
A jihar Jigawa, wani mummunan hatsarin mota da ya faru da daddare ya yi Sanadiyyar mutuwar mutane bakwai, yayin da Shugaban Karamar Hukumar Kafin Hausa ya tsira da ransa amma ya samu raunuka.
Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 9:45 na dare a Kashin Dila Junction, kan hanyar Malam Madori zuwa Hadejia, inda motar Toyota Starlet da wata Mercedes-Benz GLK suka yi mummunar karo.
Shaidun gani da ido sun ce motar Toyota Starlet na ɗauke da fasinjoji daga Hadejia zuwa Malam Madori ne lokacin da ta haɗu da GLK.
Wata majiya ta bayyana cewa motar GLK na ɗauke da Shugaban Karamar Hukumar Kafin Hausa tare da direbansa, suna kan hanyarsu daga Gumel zuwa Kafin Hausa a lokacin da hatsarin ya auku.
Rahotanni sun tabbatar cewa fasinjoji shida da ke cikin Toyota Starlet sun rasu nan take, yayin da direban motar GLK shi ma ya rasu a wajen hadarin.
Sai dai shugaban karamar hukumar ya tsira da ransa, duk da cewa ya samu raunuka, inda aka garzaya da shi asibiti domin kula da lafiyarsa cikin gaggawa.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, SP Shi’isu Adam, bai samu damar amsa kiran waya ba yayin da aka tuntuɓe shi domin jin ƙarin bayani.
Sai dai wata majiya daga hedikwatar ‘yan sanda ta tabbatar da faruwar hatsarin, tana mai cewa an buɗe bincike domin gano musabbabin lamarin.
