News
Tsananin Zafi Ya Hallaka Mutum 1,000 A Spain

Akalla mutum 1,028 suka mutu sakamakon zafi a Spain yayin da kasar ke fama da tsananin zafi da ba taba fuskantar irinsa ba tsakanin watan Janairu zuwa Yuni. Masana kimiyya sun ce yana da nasaba dasauyin yanayi
Mutane fiye da 1000 sun mutu a kasar Spain sakamakon tsananin zafi da aka fuskanta a baya bayan nan. Jami’ai sun ce kasar ta fuskanci yanayin zafi mafi tsanani wanda ba a taba ganin irinsa ba.
Cibiyar lafiya ta Carlos III a Spain ta ce an sami aukuwar mace-mace masu nasaba da yanayin zafi na mutum 1,028 a lokacin tsananin zafin a watan da ya gabata.
Adadin ya rubanya alkaluman mutum 407 da suka rasu saboda zafi a watan Junin 2025.
A ranar 23 ga watan Juni da yanayin yafin ya kai kololuwa inda mutane miliyan talatin da biyar da dubu dari bakwai kwatankwacin kashi 73 cikin dari na al’ummar Spain suka sami kansu cikin hadarin rashin lafiya saboda tsananin zafi.
