Connect with us

News

Ajiye Waya A Kan Gado A Lokacin Da Ake Caji Na Da Illa Ga Lafiya —Masani

Published

on

Screenshot 2026 06 30 152428
Advertisements
ads

Wani masanin harkokin lantarki kuma mai wayar da kan jama’a kan amfani da kayayyakin wutar lantarki, Patrick Okoye, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji cajin wayoyinsu a kan gado, filo ko ƙarƙashin bargo, yana mai cewa hakan na iya haddasa gobara tare da jefa rayuka da dukiyoyi cikin haɗari.

Okoye ya bayyana hakan ne yayin wani shirin wayar da kan jama’a kan hanyoyin amfani da kayayyakin lantarki cikin aminci da aka gudanar a ranar Asabar a birnin Awka.

Tsananin Zafi Ya Hallaka Mutum 1,000 A Spain

Ya bayyana cewa sanya waya a kan gado ko ƙarƙashin abin rufa yayin da ake cajinta na hana zafin da take fitarwa samun damar watsewa, lamarin da kan sa wayar yin zafi fiye da kima har ya kai ga haddasa gobara.

A cewarsa, haɗarin na ƙaruwa musamman a lokacin damina, saboda yawaitar tsawa da sauyin ƙarfin lantarki da ke faruwa sakamakon yawan ɗaukewar wuta da dawowarta ba tare da daidaito ba.

“Mutane da dama ba su fahimci cewa cajin waya a kan gado yana hana zafi fita yadda ya kamata, wanda hakan ke ƙara yiwuwar wayar yin zafi fiye da ƙima. A lokacin damina kuma, tsawa da sauyin ƙarfin lantarki na ƙara haɗarin aukuwar gobara,” in ji shi.

Advertisement

Masanin ya shawarci jama’a da su riƙa cajin wayoyinsu a kan teburi ko wani wuri mai ƙarfi da ba ya saurin kamawa da wuta, sannan su cire caja da zarar batirin wayar ya cika.

Haka kuma, ya yi gargaɗi kan amfani da caja marasa inganci da kuma loda filogin wuta da kayayyaki fiye da ƙarfinsa, yana mai cewa waɗannan halaye na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa gobarar lantarki.

Okoye ya jaddada cewa bin ƙa’idojin amfani da kayayyakin lantarki cikin aminci ya kamata ya zama al’adar yau da kullum domin kare rayuka da dukiyoyi.

Ya kuma yi kira ga makarantu, cibiyoyin addini, shugabannin al’umma da ƙungiyoyin matasa da su ƙara wayar da kan jama’a kan hanyoyin kauce wa haɗurran da ke tattare da amfani da kayayyakin lantarki.

A cewarsa, faɗaɗa wayar da kan jama’a na daga cikin ingantattun hanyoyin rage yawaitar gobarar da ke da alaƙa da kayayyakin lantarki.

“Ya kamata mutane su guji yin barci yayin da wayoyinsu ke caji, musamman idan suna kan gado ko ƙarƙashin bargo. A koyaushe a riƙa cajin waya a kan wuri mai ƙarfi kuma nesa da duk wani abu mai saurin kamawa da wuta. Matakan kariya masu sauƙi na iya ceton rayuka da dukiyoyi,” in ji Okoye.

Advertisement

 

 

PREMIUM TIMES 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending