News
Gwamnatin Tarayya Ta Janye Batun Maye Gurbin Kayan NYSC Da Adire
Ministan ci gaban matasa, Ayodele Olawande, ya bayyana cewa har yanzu gwamnatin tarayya ba ta amince da maye gurbin kayan masu yi wa ƙasa hidima na NYSC da atamfar Adire ba.
Ministan ya yi wannan karin haske ne bayan kalamansa da ya yi a wata hira da gidan talabijin na Channels TV da suka haifar da ce-ce-ku-ce, inda aka ruwaito cewa gwamnati ta amince da sauya Uniform din NYSC da Adire.
An Kama Jami’an NSCDC Da Wani Mutum Guda Bisa Haɗin Baki Suna Yi Wa Ƴan Bindiga Safarar Makamai
Cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Olawande ya ce an yi kuskuren fahimtar abin da ya faɗa, domin ya ambaci Adire da Ankara ne kawai a matsayin wasu daga cikin shawarwarin da ake nazari a kansu a cikin shirin sake fasalin NYSC.
Ya ce har yanzu ba a yanke hukunci kan irin atamfar da za a yi amfani da ita ba.
Ministan ya ƙara da cewa gwamnati na duba abubuwan da za su dace kuma masu kyan gani da nuna asalin Nigeriya mai ɗorewa da sauƙin amfani da rage kuɗi da kuma inganta martabar Najeriya.
Ya ce duk wata matsaya da za a ɗauka za ta kasance ne bayan kammala tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma abin da ya fi dacewa da NYSC da ƙasar baki ɗaya.
-
News4 days ago
Ƴansanda Sun Kama Ɗan Basarake Bisa Zargin Kona Wani Mutum Kan Zargin Satar Itacen Girki
-
News3 days ago
Majalisar Dokokin Kano Ta Bada Umarnin Binciken Kuɗaɗen Tsaro Na Ƙananan Hukumomi 44 Cikin Mako Biyu
-
News1 day ago
Shugaban FCAPT: Rajistar Katin Zaɓe Muhimmin Mataki Ne Wajen Ƙarfafa Dimokuraɗiyya
