Business
Matatar Mai Ta Dangote Ta Koma Siyar Da Fetur Da Dala Maimakon Naira
Matatar mai ta Dangote ta sanar da sauya tsarin karɓar kuɗin sayen man fetur da sauran kayayyakin mai, inda daga yanzu za a riƙa biyan kuɗi da dalar Amurka maimakon Naira.
Sabon tsarin ya fara aiki nan take, kuma ya shafi sayar da fetur, Gas, Dizal, man jiragen sama, ta hanyar lodin tankoki da kuma jigilar ruwa.
‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Shugaban Makaranta A Oyo
Rahotanni daga majiyoyin masana’antar sun ce an ɗauki wannan mataki ne saboda ƙarin haɗarin sauyin canjin kuɗaɗen ƙasashen waje da matatar ke fuskanta wajen sayen ɗanyen mai.
Majiyar ta bayyana cewa a yanzu matatar Ɗangote na samun mafi yawan ɗanyen man da ta ke tacewa daga NNPCL, bisa yarjejeniyar da a ke biyan kuɗinta da dala, yayin da har yanzu a ke sayar da yawancin man da a ka tace a cikin gida da naira.
An ce wannan bambanci tsakanin sayen ɗanyen mai da dala da kuma sayar da man da naira ya jefa matatar cikin haɗarin asarar kuɗi sakamakon canjin farashin musayar kuɗi, lamarin da ya sa aka yanke shawarar komawa amfani da dala wajen sayar da kayayyakin.
Wata majiya ta ce daga yanzu dukkan sayar da fetur, dizal da man jiragen sama za su kasance ne da dala, kuma an aika sanarwar ga dillalan da ke ɗaukar mai daga matatar.
Jami’an matatar sun kuma bayyana cewa ci gaba da sauyin farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya da rashin tabbas a kasuwar canjin kuɗaɗen waje ta Najeriya sun taka rawa wajen ɗaukar wannan mataki.
Sun ƙara da cewa matatar na buƙatar fiye da tankokin jiragen ruwa goma sha biyar na ɗanyen mai a kowane wata domin gudanar da ayyukanta, amma NNPCL na samun wahalar samar da ko tankoki uku da ake biya da naira a ƙarƙashin tsarin musayar naira da ɗanyen mai.
Masana tattalin arziƙi na ganin cewa wannan sabon tsari na iya yin tasiri ga farashin mai, kuɗin sufuri da kuma ƙara buƙatar dala a ƙasar, musamman ganin cewa Matatar Dangote na daga cikin manyan masu samar da tataccen mai a Najeriya.
Sun yi gargadi cewa wannan mataki zai ƙara buƙatar dala a Najeriya, lamarin da ka iya ƙara raunana darajar naira idan ba a samu mafita ba.
-
News7 days ago
Hukumar Kula Da Harkokin Shari’a Ta Tilasta Wa Alƙali Ritaya Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Naira 250,000 A Kano
-
News7 days ago
Wasu Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Tare Da Kona Gawarsa Kan Zargin Satar Babur A Kano
-
News7 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Kama Mahaifin Prince Adeyemi Adeniyi, Mutumin Da Ake Zargi Da Kafa Hukumar Bogi
