News
Maulidi Na Taimakawa Wajen Tunar Da Al’umma Halayen Annabi —Malam Ibrahim Khaleel
Daga Abubakar Zaharadden Kano
Fitaccen Malamin Addinin Musuluncin nan a Najeriya kuma shugaban Majalissar Malamai ta jihar Kano Sheikh Malam Ibrahim Khaleel, ya bayyana tasirin kasancewa a tarukan Maulidi musammanma wanda ake ambato da fadan halayen Manzon ALLAH (S.A.W) kawai.
Malam Khaleel, ya bayyana hakan a wani taron Maulidin da aka gudanar a Kano wanda wani bawan ALLAH Mahmud Adahama, ke shiryawa kowacce Shekara a gidansa da ke Unguwar G.R.A.
Dr Muhammad Hamisu UK Ya Bayyana Shirin Tallafawa Matasa Da Mata A Gwale
A cewar Malam Khaleel, shirya tarukan Maulidi irin haka yana kara tasiri wajen tunasar da mutane irin halayen Annabi Muhammad (S.A.W), musamman ma idan akayi la’akari da yadda nutsuwar taron take ruɓanya idan aka kwatanta da taron bara.
Sheikh Khaleel, ya kuma kara fito da girman ladan da wadanda ke shirya taron Maulidi irin haka za su samu a wajen ALLAH madaukakin Sarki.
Shin ko me yasa Al’ummar musulmin ke shirya tarukan Maulidi da sauran tarukan da ake ambaton ALLAH da kuma Manzon ALLAH (S.A.W) ?
Mahmud Sa’eed Adahama, shi ne wanda ya shirta taron na bana. yakuma bayyana cewa a hidimtawa Annabi muhammad (SAW) babu fashi saboda ashirye yake da ya sadaukar da duk abunda ya mallaka wajen hidimtawa annabi muhammad (SAW)
mahmuda sa’eed Adhama, yakara da cewa akowace shekara dubban jama’a daga ko ina suna dakon ranar da ze gudanar da maulidin gidansa saboda al’umma suna gamsuwa da abunda akeyi na koyarwa Annabi muhammad (SAW)
Shima a nasa bangaren da yake jawabi a gefen taron, Yariman Kano Umar Ado Bayero, ya bukaci Al’ummar jihar Kano da su rika shirya tarukan da za’a dinga fadar halayen Manzon ALLAH irin haka musamman ma idan sun samu dama.
Da yake jawabin godiya ga wadanda suka halarci taron, Dattijo Sa’eed Adahama, ya bayyana jin dadinsa bisa yadda Maulidin ya samu halartar dumbin mutane da dama.
dakuma Addu’ar allah yahadasu a ladan bakin daya
Za dai a iya cewa taron Maulidin wanda shine karo na 18, ya sha bam-bam da irin na shekarar Bara musamman wajen ganin nutsuwa a fuskokin mahalartan, inda daga bisani aka rufe taron da Addu’a tare da fatan samun zaman lafiya a jihar Kano dama kasa baki Daya.
