Connect with us

Labarai

‎Fasinja Ya Rasu Bayan Fara Rashin Lafiya A Jirgin Kenya Airways Da Ke Kan Hanyar Zuwa Legas

Published

on

kenya airways
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Wani fasinja ya rasu bayan ya fara rashin lafiya a cikin jirgin Kenya Airways (KQ) da ke kan hanyarsa daga Nairobi, babban birnin Kenya, zuwa Legas, cibiyar kasuwancin Nijeriya, ranar Talata, 6 ga Oktoba, kamar yadda kamfanin jiragen ya sanar a wata sanarwa ranar Laraba.

A cewar Kenya Airways, fasinjan ya daina motsi kimanin mintuna 20 kafin jirgin ya sauka a Legas. Matsalar lafiyar ta faru ne da misalin ƙarfe 9:20 na dare agogon Nijeriya.

Ƙungiyar Academic Cycle Ta Jaddada Goyon Bayanta Ga Gwamnatin Kano Kan Bunƙasa Harkar Ilimi A Jihar 

Kamfanin ya ce ma’aikatan cikin jirgin sun ba fasinjan agajin farko bisa horon da suka samu, tare da bin matakan gaggawa da aka tanada.

Jirgin ya sauka a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Murtala Muhammed da ke Legas da ƙarfe 9:41 na dare, inda ma’aikatan lafiya ke jiransa.

Bayan ƙarin bincike da duba lafiyarsa, ma’aikatan lafiya sun tabbatar da cewa fasinjan ya rasu..

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending