Labarai
An Hallaka Wani Ma’aikacin Wutar Lantarki Kan Yanke Wa Wani Gida Wuta

An kashe wani ma’aikacin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Benin (BEDC), Oscar Udoka Eze, mai shekaru 38, bayan wasu mutane sun kai masa hari da wuƙa a Jihar Delta.
An kashe ma’aikacin ne bisa zargin cewa ya yanke wa wani gida wutar lantarki saboda bashin kuɗin wuta na Naira 300,000.
Ba A Buƙatar Rahoton Jami’an Ƴansanda Kafin Duba Wanda Aka Harba —Sufeto-Janar
Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne ranar Litinin, 16 ga Nuwamba, 2026, a yankin Idumobi da ke Umunede, yayin da marigayin ke gudanar da aikinsa.
Muƙaddashin Manajan Daraktan BEDC, Jonathan Lawani, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce Eze ya yanke wutar gidan wani kwastoma saboda bashin da ake bin sa.
Ya ce bayan yanke wutar, wasu mutanen gidan sun bi ma’aikacin zuwa wani gida, inda suka kai masa hari da wuƙaƙe da adduna.
Lawani ya yi Allah-wadai da kisan, yana mai cewa ma’aikacin bai yi gardama ko tsokanar waɗanda suka kai masa harin ba, illa dai yana gudanar da aikinsa na yau da kullum.
Ya kuma bayyana cewa jami’an tsaro sun kama wasu mutane da ake zargi da hannu a kisan.
Muƙaddashin manajan daraktan ya yi kira ga gwamnatin Jihar Delta da ta ƙara ƙaimi wajen samar da tsaro domin kare ma’aikatan kamfanonin wutar lantarki yayin gudanar da ayyukansu.
Haka kuma, kamfanin BEDC ya buƙaci hukumomin tsaro su gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da tabbatar da cewa duk waɗanda aka samu da hannu a kisan sun fuskanci hukuncin da ya dace a gaban kotu.
