News
Mu na tare da Russia a yaƙin da ta ke da Ukraine — China
Daga kabiru basiru fulatan
Kasar China ta nuna goyon bayan ta Russia a mayar da ta yi wa Ukraine a halin yanzu.
Ministan Harkokin Waje na China, Wang Yi ne ya baiyana hakan.
A cewar sa, China da Russia kawaye ne kuma duk da ƙurar da ke tashi a duniya, wannan kawancen nasu yana nan daram.
“Kuma za mu ci gaba da bunƙasa haɗin gwiwar mu a zamanin da a ke ciki,” in ji Wanga, yayin da ya ke amsa tambaya a kan takunukuman da ƙasashen yamma su ka ƙaƙaba wa Russia a kan mamayar da ta yi wa Ukraine.
Wang ya kuma suffanta Russia da China a matsayin maƙota na kusa kuma ƙawaye ne masu son ci gaban juna, inda ya kira alaƙar ta su a ɗaya da ga cikin mafi girma a duniya.
Ya ce kawancen su ba wai al’ummar ƙasashen biyu kawai zai amfana ba, zai samar da zaman lafiya da ci gaba a duniya.