News
Rasha ba za ta manta sojojinta da suka mutu a fagen yaƙi ba – Putin
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaba Rasha Vladimir Putin ya yi alƙwarin cewa Rasha ba za ta taɓa mantawa da sojojinta waɗanda ke filin daga da waɗanda suka mutu ba.
Mista Putin na wannan kalamai ne yayin da yake ganawa da uwayen sojojin da ƙasar da aka tura yakin Ukraine.
Dole ne Matasan Najeriya su yi adawa da masu kawo cikas ga makomarsu – Obasanjo
Ya gaya wa matan cewa yana jin zafi tare da waɗanda suka rasa ‘ya’yansu a yaƙin.
‘’Ina so ku sani cewa ni da kaina da gwamnatina muna jin zafin wannan rashi tare da ku, kuma mun san cewa ba a bin da zai iya maye gurbin rashin ɗa musamman ma ga uwa’’, in ji mista Putin.
Wannan dai shi ne karon farko da fadar gwamnatin Rasha ke ƙoƙarin nuna cewa shugaban Putin ya damu da sojojin da kuma iyalansu.
A ’yan kwanakin nan mataye da ‘yayansu sun riƙa sanya sakonni na bacin rai cewa an tura mazaje da ‘yayansu fagen daga ba tare da horo ko isassun kayyyakin yaki ba.
