News
Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Da Kafa Hukumar Daukar Ma’aikatan Kananan Hukumomi
Majalisar dokokin Jihar Kano ta amince da kafa sabuwar hukuma da za ta kula da daukar ma’aikata da gudanar da harkokin ma’aikatan kananan hukumomi a fadin jihar.
An amince da dokar ne a zaman majalisar na ranar Litinin 2 ga watan Maris 2026, a zauren Majalisar Dokokin Jihar Kano.
Sabuwar hukumar za ta rika daukar ma’aikata daga mataki na daya zuwa na bakwai, tare da kula da ladabtarwa, karin girma, sauya wurin aiki, horaswa da kuma inganta kwarewar ma’aikata a kananan hukumomi.
A lokaci guda, majalisar ta amince da gyaran dokar ma’aikatan majalisar dokoki, inda ta samar da mukamin mataimakin akawun majalisa na biyu domin karfafa tsarin gudanarwa.
Da yake karin bayani, Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Husaini Dala, ya ce hukumar za ta kasance karkashin jagorancin kwararren ma’aikacin gwamnati da ya yi ritaya, wanda matsayinsa na albashi bai gaza mataki na 15 ba.
Ya kara da cewa za a samar da kwamitocin gudanarwa a karkashin hukumar domin saukaka tafiyar da ayyukanta yadda ya kamata.
Matakin, a cewar majalisar, na daga cikin kokarin da gwamnati ke yi na inganta tsarin daukar ma’aikata da karfafa gudanar da ayyukan kananan hukumomi a jihar.
-
News1 day ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
