News
Yara Huɗu Sun Nutse Ruwa A Edo
Yara biyu sun mutu yayin da wasu biyu suka tsira bayan sun nutse a wani wurin tara ruwan ambaliya da ke titin Erediauwa, kusa da Sapele Road, a ƙaramar hukumar Ikpoba-Okha ta Jihar Edo.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, kamar yadda wata majiya ta shadawa Jaridar Punch
Wani shaidar gani da ido, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa yara huɗu ne suka je wasa a kusa da wurin da gwamnatin jihar ta ware domin tara ruwan ambaliya.
Yara Biyu Sun Nutse Ruwa A Edo
A cewarsa, yayin da suke wasa ne suka zame suka fada cikin ruwan da ke cike da laka, lamarin da ya janyo nutsewar su.
> “Kafin agajin gaggawa ya iso, yara biyu sun riga sun rasu, yayin da aka samu nasarar ceto sauran biyun cikin mawuyacin hali,” in ji majiyar.
An ce an zakulo gawarwakin yaran biyu daga cikin ruwan, yayin da aka garzaya da sauran biyun zuwa wani asibiti da ke kusa domin kula da lafiyarsu.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Edo, Eno Ikoedem, ta tabbatar da faruwar lamarin.
Ta ce an tura jami’an ceto nan take bayan samun rahoton aukuwar lamarin, inda aka tabbatar da mutuwar yara biyun a wurin da abin ya faru.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a bayyana karin bayani kan halin da sauran yaran biyu da aka ceto suke ciki ba.
-
News5 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News4 days ago
ICPC Ta Wanke Femi Gbajabiamila Daga Zargin Badakalar Hukumar Bogi
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Dakile Yunkurin Sace Jariri Da Wasu Ma’aikatan Asibiti A Jigawa
