News
Kashi 30% Ne Kawai Na Yaran Daya Kamata Suje Makaranta Suke Zuwa A Arewacin Najeriya —Farfesa Salisu Shehu
DAGA UMAR IBRAHIM MUHD
Babban Sakataren Hukumar Bunkasa Harkokin Ilimi ta Kasa, Farfesa Salisu Shehu, ya ce kashi 30 cikin 100 kacal na yaran da suka kai shekarun zuwa makaranta ke zuwa Arewacin Najeriya.
Ya bayyana hakan ne a yayin taron Ramadan karo na 10 da Islamic Forum of Nigeria ta shirya a Kano.
Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Da Kafa Hukumar Daukar Ma’aikatan Kananan Hukumomi
Farfesan ya ce sama da yara miliyan 20 ne a Najeriya ba sa zuwa makaranta, yana mai danganta hakan da matsalolin tsaro da suka hada da hare-haren ’yan bindiga a Arewa maso Yamma da kuma rikicin tayar da kayar baya a Arewa maso Gabas, lamarin da ya haddasa rufe makarantu a wasu jihohi.
Ya kuma nuna damuwa kan karancin malamai sakamakon ritaya, sauyin aiki da rasuwa, yana mai gargadin cewa rashin ilimi na kara haddasa rashin zaman lafiya da ta’addanci.
Farfesa Shehu ya bukaci gwamnonin Arewa su ayyana dokar ta-baci a bangaren ilimi, su kuma kara zuba jari domin farfado da tsarin koyarwa. Ya ce kasashe kamar Bangladesh da Malaysia sun taba fuskantar irin wannan kalubale, amma suka samu ci gaba ta hanyar hadin gwiwar gwamnati da al’umma.
Ya kuma soki abin da ya kira fifita wasu abubuwa marasa muhimmanci a kan ilimi, yana mai cewa ya kamata a ba ilimi fifiko domin ceto makomar matasa.
A nasa jawabin, Alhaji Ibrahim Ado Kurawa ya danganta tabarbarewar tsaro da sauyin yanayi da rikicin manoma da makiyaya, yana mai cewa hakan na kara jefa yankunan Arewa cikin talauci da fatara.
Shi kuma Farfesa Kabiru Isa Dandago ya ce talauci, rashin aikin yi da tsadar rayuwa na daga cikin manyan kalubalen da ke barazana ga ci gaban yankin.
Shugaban Majalisar Malamai ta Kasa, Malam Ibrahim Khalil, ya jaddada muhimmancin shugabanci mai gaskiya da kishin kasa, yana mai cewa hakan ne mafita ga kalubalen da Arewacin Najeriya ke fuskanta.
Taron ya kuma samu halartar manyan baki da dama, ciki har da Sarkin Rano, Amb. Muhammad Isa Umaru.
-
News5 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News4 days ago
ICPC Ta Wanke Femi Gbajabiamila Daga Zargin Badakalar Hukumar Bogi
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Dakile Yunkurin Sace Jariri Da Wasu Ma’aikatan Asibiti A Jigawa
